Bidiyo. Adam A Zango da Zee Pretty sun bude wa Buhari wuta akan kisan yan Arewa.

Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood Adam A Zango, tare da fitacciyar jaruma Zee Pretty, sun rufe ido sun bude wa shugaban kasar Najeriya wuta.

Jaruman Kannywood sun fara fusata akan halin da kasar Najeriya take ciki, musamman bangaren Arewacin kasar. Inda wasu daga cikin jarumai suka fara bude baki, domin shugabanni su gaggauta daukar mataki.

A safiyar yau Juma’a ne dai al’umma da dama daga Arewacin Najeriya suka bayyana fushin su a fili, akan halin rashin tsaro, da firgici da rashin kwanciyar hankali da ake fama da su a kasar.

Inda a yau jama’a suka fito zanga-zanga domin bayyana wa duniya halin da Najeriya take ciki, musamman bangaren Arewa. Domin ta haka ne kadai Talaka yake da ikon bayyana fushin sa zuwa ga Gwamnati.

Daga cikin jaruman Kannywood akwai mutane da dama suka wallafa zafafan sakonni akan shafukan su zuwa ga Gwamnatin Najeriya, kamar irin Hadiza Aliyu Gabon, Zee Pretty Adam A Zango, da dai sauran su.

Sai dai wani abin takaicin Kuma shine, duk lokacin da aka yi irin wannan zanga-zanga domin neman mafita, sai kaga Gwamnati ta dan yi wani yunkuri kadan. Amma da zarar komai ya lafa, sai kawai kaga an koma gidan jiya.

To abin tambaya a nan shine, shin wai ita Gwamnatin bata kishin kasar ta da al’ummar ta ne? Shin Gwamnati bata jin ciwon jinin mutane da ake zubarwa a kowacce rana? Idan kuma tana jin kishin al’ummar tata, to don Allah mai yasa kullum lamarin yake ‘kara tabarbarewa?

To a halin yanzu dai zakuji wani zazzafan sako da jaruman Kannywood Adam A Zango da Zee Pretty suka aika, kai tsaye zuwa ga shugabannin Najeriya, akan rayukan da ake ta kashewa a Arewacin kasar.

Yanzu kuma ga bidiyon nan a kasa, inda zaku fara jin maganar Zee Pretty. Daga bisani kuma sai kuji abinda Adam A Zango ya fada.

Leave a Comment