Bidiyo. Malaman Addini da jaruman Kannywood sun bude wa Buhari wuta akan kisan yan Arewa.

Jarumai da Malamai suma sun bada tasu gudunmuwar akan halin da ake ciki kashe-kashen bayin Allah a Arewacin Nigeria.

Hakika zamu iya cewa a wannan karon Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sha sakonni daga kowanne bangare.

Domin kuwa yau kafafen sadarwa gaba ‘daya sun cika da zafafan sakonni zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Kuma kowa yana aika sakon na shi ne a cikin fushi. Saboda kashe mutanen da kullum ake yi a Arewacin Nigeria, ya wuce gona da iri.

Zamu iya cewa kusan kowa a masana’antar Kannywood ya wallafa wannan abin alhini a kan shafin sa na sadarwa, domin bada tasa gudunmuwar.

Sannan kuma suma Malaman Addini kamar su Shek Muhammad Nuru Khalid wanda ake wa lakabi da “Digital Imam”. Da Shek Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo da sauran su. Duk sun wallafa magan-ganu akan al’amarin.

Yanzu kuma zamu saka muku faifan Bidiyo, domin kuji, kuma kuga abinda malaman da jaruman suka fada.

Leave a Comment