Bidiyo. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Masu garkuwa sun tare mahaifiyar jarumar Kannywood.

Har yanzu dai tsoro da firgici da tashin hankali suna ‘kara hauhawa a zukatan mutanen Najeriya. Musamman ma ‘bangaren Arewan ‘kasar.

A daren jiya ne masu garkuwa da
mutane a kan hanyar Kaduna suka tare mutane, ciki harda mahaifiyar 'daya daga cikin jaruman Kannywood. Wato Samha Nura M Inuwa.

Kuma masu garkuwar sun tare su ne a lokacin da suke 'kokarin shiga Kaduna daga jihar Kano.

Samha M Inuwa ta wallafa wannan bidiyo ne akan shafin ta na Tiktok, inda take kuka take neman addu'ar 'yan uwa da abokan arziki, akan abinda ya faru da mahaifiyar ta ta.

Samha ta fada cewa a lokacin da masu garkuwar suka tare motar da mahaifiyar ta ke ciki. Sai mutanen cikin motar suka fito a 'dimauce, inda suka ruga da gudu cikin daji, kuma abin ya faru ne a cikin dare.

To a dai wannan lokacin ne sai mahaifiyar Samha ta kira waya ta sanar da halin da suke ciki a cikin tsakar daji. Wato irin gurin da Bahaushe yake cewa "Ba gida gaba, ba gida baya".

Hakika wannan tashin hankalin ya kai tashin hankali. Domin shine yasa Samha ta fito tana ta kuka, kuma take neman addu'ar mutane.

Yanzu kuma ba tare da 'bata lokaci ba. Zamu saka muku bidiyon wannan jaruma wato Samha Nura M Inuwa, inda take bada labarin yanda abin ya faru.

Daga bisani kuma zaku 'kara ganin wani bidiyon a 'kasa, wanda jarumar ta kuma dawowa ta bada sabuwar sanarwa mai dadi.

To yanzu dai ga sakon farko da Samha M Inuwa ta fara fitarwa akan halin da mahaifiyar ta ke ciki, wanda ya tada hankalin mutane.

To yanzu kuma ga sakon da Samha ta fitar daga baya, wanda ya faranta wa mutane rai.
Muna rokon Allah ya kawo mana 'dauki a Najeriya, musamman 'bangaren Arewacin 'kasar. Kuma dukkan masu hannu a cikin wannan al'amari, Ya Allah Kai ka san su, kuma Kai ka san inda suke. Ya Allah kayi musu hukuncin da yafi dacewa da su. Amin summa amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.