Masu garkuwa a Nigeria sun bayyana dalilin da yasa bazasu daina satar mutane ba.

Wani 'kasungurmin mai garkuwa da mutane a jihar Zamfara, ya bayyana makasudin abinda yasa bazasu daina satar mutane a Najeriya ba.

Wannan tashin hankali da mai yai kama? A lokacin da ake tsaka da alhinin abubuwan da suke faruwa a Arewacin Najeriya, na yin garkuwa da mutane da kashe-kashen bayin Allah. Sai gashi kuma wani mai garkuwar ya 'kara yin wata magana da ta 'kara firgita mutane.

Shin wai masu garkuwa sunfi 'karfin Gwamnatin Najeriya ne? Idan ba haka ba to mai yasa har yanzu an kasa shawo kan matsalar su?

A halin yanzu dai sakonnin Yan Najeriya sun gama cika kunnen shugaban 'kasa Muhammadu Buhari. Domin kuwa kusan kowa a wannan lokacin ya bayyana 'bacin ran sa akan abubuwan dake faruwa a Arewacin Najeriya.

Malaman Addini, jaruman Kannywood, talakawa da masu kudi, yara da manya. Kusan kowa ya aika sakon sa ga shugaban 'kasa a kan wannan tashin hankali da ake ciki.

Sai dai su masu garkuwa da mutane da alama ko a jikin su. Wato duk wadannan abubuwan da suke faruwa su babu abinda ya dame su, domin kuwa suna nan suna ci gaba da aiwatar da aikin su.

Shafin DW ya tattauna da wani mai garkuwa da mutane a jihar Zamfara. Wanda yanzu zamu kawo muku tattaunawar domin kuji irin abinda wannan mai garkuwa ya fada.

Ga tattaunawar nan a 'kasa, wadda wakilin DW ya tattauna da mai garkuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.