Bidiyo. Aljanin ‘barawo ya shiga hannun ‘yan sanda a jihar Kano.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano tayi nasarar kama wasu shahararrun 'barayi a jihar Kano, wadanda suka dade suna addabar al'umma.

Daga cikin 'barayin akwai wani mai suna Aljan, wanda yai 'kaurin suna waje sata, da 'kwacen adaidaita sahu wato Keke Napep.

Hakika shima wannan al'amari na 'kwacen wayoyi da Adaidaita sahu a kan tituna, yana 'daya daga cikin abubuwan da suka damu mutane a Arewacin Najeriya.

Saboda kusan kullum sai jami'an tsaro sun fitar da sanarwa cewa sun kama 'barayin. Amma kuma duk da haka matsalar bata kare ba, domin kuwa 'barayin suna nan suna ci gaba da aiwatar da aikace-aikacen su.

Amma tabbas zamu iya jinjina wa 'yan sanda a jihar Kano, a kan 'kokarin da suke yi na rage irin wadannan bara gurbin, a cikin al'umma.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shine ya sanar da wannan gagarumar nasara da aka cimma, ta kama wadannan 'barayi.

Kiyawa ya tattauna da wadannan 'barayi, inda suka bayyana irin dabarun da suke amfani dasu wajen sace Mashina, da Adaidaita sahu, da kuma 'kwacen wayoyi.

Yanzu kuma zamu saka muku bidiyon, domin kuga yanda aka tattauna da wadannan 'barayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.