Matar Adam A Zango ta farko, ta dawo fim.

Amina matar Adam A Zango ta dawo fim, bayan shekaru 13 da ta bar harkar.

Tsohuwar matar jarumi Adam A Zango, wato wadda ya fara aura a rayuwar sa mai suna Amina, ta dawo harkar fina-finan Kannywood.

Amina dai itace wadda ta fara karbar sadakin Adam A Zango, inda ta haifa masa dan sa na farko mai suna Haidar. Wannan dalili ne ma yasa ake wa Amina lakabi da Maman Haidar.

Amina dai ta fara harkar fina-finai ne tun wajajen sherar 2000, inda kuma ta zama matar Adam A Zango a shekarar 2007.

Amina ta haifi Haidar, wato dan Adam A Zango na farko a shekarar 2008, inda Allah Ya kawo karshen zaman su a matsayin ma’aurata bayan watanni 5 da haihuwar Haidar.

Mutane sun fahimci cewa Amina ta dawo harkar fim ne, bayan da aka gan ta tana taka rawa a wani shiri mai dogon zango, wanda ake haskawa a tashar Talabijin ta Arewa24, mai suna Gidan Danja.

Jarumar, wadda ta kasance haifaffiyar jihar Kaduna, ta fada cewa a yanzu ta dawo harkar fina-finai da karfin ta, fiye ma da yanda take a baya. Inda ta tabbatar da cewa za’a ci gaba da damawa da ita, har sai taga abinda ya ture wa Buzu nadi.

Amina tace. “A matsayi na ta uwa, kuma bazawara, dawowa ta harkar fim ba abu ne mai sauki ba, bayan wadannan tsawon shekaru da na kwashe bana cikin harkar, amma dai inada cikakken karfin gwiwar cewa zan iya, saboda taka rawa a fina-finai shine abinda nake da burin yi, don haka kuma shine abinda zan yi.

A halin yanzu dai masoyan wannan jaruma suna ta yabawa da rawar da take takawa a cikin fim ‘din mai dogon zango na Gidan Danja.

3 thoughts on “Matar Adam A Zango ta farko, ta dawo fim.”

  1. Please let me know if you’re looking for a article writer for your weblog. You have some really good articles and I feel I would be a good asset. If you ever want to take some of the load off, I’d absolutely love to write some material for your blog in exchange for a link back to mine. Please blast me an e-mail if interested. Many thanks!

    Reply

Leave a Comment