Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Allah Ya karbi rayuwar Sani SK.

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un. Jarumi Sani Garba SK ya amsa kiran Ubangiji, a yammacin wannan rana ta Laraba.

Hakika dukkan mai rai mamaci ne, wannan magana ce wadda bata bukatar fassara, domin kuwa mutuwa wa'azi ce da take faruwa a zihiri kowa yana kallo.

Yanzu muka samu labarin mutuwar jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Sani Garba SK, Inda yanzu hakama labarin mutuwar tasa har ya fara yawo a kafafen sadarwa na zamani.

Rayuwa kenan. Sani SK yasha fama da rashin lafiya, wanda a kwanakin baya ya fito yana neman taimakon al'umma, akan rashin lafiyar da yake fama da ita.

Wanda a lokacin ne aka tura masa wasu yan kudade da zai amfani da su wajen kula da lafiyar tasa. Harma daga baya jarumin ya sake fitowa yai wa mutane godiya akan taimakon da aka tura masa.

Sannan kuma idan baku manta ba, a kwanakin baya ma an yada labarin cewa SK ya rasu, har ma jarumin ya fito yayi magana cewa yana nan a raye.

Allahu Akbar duniya. To kamar yanda kowa yake jiran lokacin mutuwar sa. Shi Sani Garba SK lokacin sa yayi. Domin kuwa tuni ya amsa kiran Ubangiji sa.

Shafin BBC Hausa ya wallafa wannan labari na mutuwar SK. Sannan kuma manyan jarumai suma sun wallafa labarin, kamar su Ali Nuhu, Aminu S Bono da sauran su.

Muna fata Allah Yaji 'kan Sani SK Yai masa Rahma. Kuma ya kyauta namu zuwan. Amin summa amin. Daga baya zamu kawo muku cikakken labarin.

Kuci gaba da kasancewa da shafin Mujallar Hausa, domin sanin dukkan abubuwan da suke kai, kawo, na al'amuran yau da kullum. Musamman al'amuran da suka shafi Masana'antar Kannywood.

One Reply to “Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Allah Ya karbi rayuwar Sani SK.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.