‘Yan Fim Ba Jahilai Bane. Cewar Jaruma Ummi Abdulwahab.

Jarumar Kannywood Ummi Abdulwahab, wadda akafi sani da Ummi El-Abdul tayi zazzafan martani akan masu kallon 'yan fim a matsayin jahilai.

To wannan dai wata siffa ce da wasu suke kallon 'yan fim da ita. Kuma abin ya 'dakko asali ne, tun lokacin da aka fara harkar ta fina-finai.

Wanda a wancen lokacin tabbas akwai 'karincin masu ilimi a cikin harkar. Amma kuma yanzu zamu iya cewa wannan magana ta zama tarihi.

To kasancewar duk al'ummar da aka siffanta ta da "Jahilci" bata jin dadi. Shiyasa sau da yawa 'yan fim 'din su kan fito suyi martani ga masu yi musu kallon jahilai.

To a nan ma dai an kuma. Inda 'daya daga cikin jarumai mata a cikin a masana'antar ta Kannywood mai suna Ummi Abdulwahab, wadda ake kira Ummi El-Abdul, ta fito ta nuna fushin ta, kuma tayi martani akan masu yi musu kallon jahilai.

Ummi ta tabbatar da cewa Tabbas 'yan fim ba jahilai bane, sunada ilimin su. Saboda haka ne ma har suke yin fadakarwa.

Jarumar tayi wannan martani ne a wata tattauna da tayi da wakilin jaridar Dimokradiyya, dangane da irin kallon da ake musu na jahilai, kuma ake zargin su da cewa jahilcin ne ma yasa suke fitowa su aikata abinda suka ga dama, ba tare da jin kunya ko kuma sanin ya kamata ba.

Ummi El-Abdul tace “Ai shi ilimi ba ya 'buya, kuma ana gani a cikin sana'ar da mu ke yi, don haka mu ba jahilai ba ne muna da ilimin mu, don haka a daina yi mana kallon Jahilai”

El-Abdul ta 'kara da cewa “Kowa da ka gani da yadda Allah ya tsara masa rayuwar sa, to mu ma haka rayuwar mu ta kasance. Kuma yanzu da na ke yin harkar fim, idan Allah ya kawo mini miji na yi aure, shikenan sai dai a rinka labarin na taba yin fim a baya".

A 'karahen tattaunawar ne kuma Ummi tayi addu'ar Allah Yasa ta gama da harkar fim lafiya, sannan kuma ta samu miji tayi aure.

To Ummi, muna fata Allah Ya cika miki wannan buri naki, tare da duk wadanda suke cikin harkar ta fina-finai. Amin summa amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.