Bidiyo. Allahu Akbar duniya. Anyi jana’izar Sani Garba SK.

Anyi jana'izar Marigayi Sani Garba SK
a safiyar yau Alhamis, wanda Allah Yai masa rasuwa a daren jiya Laraba. Wato sai da ya samu kwana 'daya sannan akayi jana'izar tasa. Irin abinda a Hausa ake kira "Kwanan Keso".

A jiya ne dai wannan abin alhini ya faru, wato na mutuwar jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wato Sani Garba SK. Wanda Allah Ya karbi rayuwar sa bayan doguwar jinya da ya sha.

To a halin yanzu dai anji jana'izar
wannan bawan Allah wato Sani SK, wanda izuwa yanzu har an kaishi makwancin sa. Kuma anyi jana'izar ne da 'karfe 9 na safiyar yau Alhamis.

Shafin BBC Hausa ya ziyarci gurin jana'izar mamacin, inda yanzu zamu saka muku abinda suka 'dakko daga gurin jana'izar ta marigayi Sani Garba SK.

Muna addu'ar Allah Yai Sani Garba SK Rahma, Ya yafe masa kurakurensa. Mu kuma idan tamu tazo, Allah Yasa mu cika da imani, Amin summa amin.

Yanzu kuma ga yanda jana'izar ta Sani SK ta kasance.

Leave a Reply

Your email address will not be published.