Bidiyo. An fara dakko hanyar gyara Najeriya.

Inda rai da rabo inji Bahaushe, Wasu alamomi sun nuna cewa yanzu an fara dakko hanyar gyara Najeriya. Lamarin da aka fara fidda rai.

Hakika wasu zasuyi mamakin wannan magana da muka fada cewa “An dakko hanyar gyara Najeriya” domin kuwa mutane sun fara cire rai da cewa Najeriya zata gyaru.

Hausawa na cewa “Ta inda aka hau, ta nan ake sauka” wato dai shugabannin da talakawa suke ba wa kuri’a, sune dai zasu yi hubbasa wajen kawo wannan gyara.

To yanzu zamu iya cewa Alhamdu Lillah, domin kuwa wasu daga cikin shugabannin Najeriya sun fara bude baki suna fadar gaskiya.

Hakika idan shugabannin Najeriya suka fara magana ta gaskiya da tsoron Allah, to wannan kadai ya isa yasa a gane cewa yanzu fa kida ya canja, don haka muna sa rai itama rawa kwanan nan zata canja.

Mutane suna zabar shugabanni ne domin su tsaya musu akan duk wani al’amari da ya shafi Gwamnati. Amma kuma a Najeriya mafi akasari, shugabannin suna cika aljihun su ne da kudaden talakawa.

Yanzu dai masu wakiltar talakawa a dakin taro na kasar, wato “National Assembly” sun fara cire tsoro akan fadar gaskiya.

Sanata Ali Ndume, ya bayyana wani al’amari akan wannan kasa ta Najeriya, wanda ya ba wa mutane karfin gwiwa akan cewa an fara samun canji.

Yanzu kuma zamu kunna muku bidiyon, domin kuji wannan magana da Sanata Ali Ndume ya fada.

Leave a Comment