Bidiyo. Buhari ya janyo wani sabon abun cecekuce da zage-zage.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kuma janyo wani babban abin magana, wanda ya janyo mutane sukai ta zage-zage da bakaken maganganu.

Har yanzu dai mutane suna taci gaba da bayyana bacin ran su akan yanda Buhari yake tafiyar da tsarin mulkin Najeriya.

Kuma yanda ake ta kashe mutane ba dare ba rana a kasar ta Najeriya, musamman ma bangaren Arewacin kasar, shine yasa kowa ya fito ya bayyana rashin jin dadin sa, inda ake ta aika wa shugaban kasa sako.

Sai dai abinda yake bawa mutane mamaki shine, mai yasa haryanzu Gwamnati taki daukar wani kwakkwaran mataki akai.

Domin kuwa duk wadannan abubuwan da suke faruwa, shi dai shugaban kasa yana nan yanata hawa jirgi yana tafiya kasashe daban-daban, domin cimma wasu bukatu na daban.

To a yau ma dai tuni shugaban kasar na Najeriya ya hau jirgi ya shilla zuwa kasar Turkiyya, domin halartar wani taro.

A wannan tafiya zuwa kasar Turkiyya, Buharin ya tafi ne tare da matar sa wato A’isha Buhari, da Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, da kuma Ministan tsaro, wato Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya.

To a dai kan wannan tafiye-tafiye na shugaban kasa Buhari, shine yasa mutane suka shiga cecekuce da bakaken maganganu, akan shugaban kasar.

A cikin haka ne kuma wani fitaccen mai wallafa maganganu a shafukan sadarwa, wato Young Uztaz, ya kawo wata shawara da yake ganin idan an bita za’a iya samun kyakkyawar mafita.

Leave a Comment