Sarkin Kano Aminu Ado zai angwance da tsohuwar budurwar sa.

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yana shirin angwancewa da tsohuwar budurwar sa mai suna Hajiyayye, yar unguwar Dorayi.

Mafi akasari, a bisa al’adar sarakuna, sunayin mata 4, wasu sarakunan ma har da kwarkwarori. Amma shi Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya kasance yanada mata 1 tal a rayuwar sa, wadda har izuwa yanzu yake tare da ita, wato bai ‘kara aure ba.

Jaridar “Daily Nigerian” ta tabbatar da cewa, majiyar ta ta bayyana cewa, tuni aka fara shirye-shirye, don tattaunawa da waliyyan amarya, domin a tsaida lokacin ‘daurin aure.

Sannan kuma majiyar ta kara da cewa an sha saka lokacin auren amma ana dagawa. Saboda a baya anso ayi bikin ne ba tare da an gudanar da shagulgulan biki na al’ada ba, wato irin wadanda ake yi a gidan sarauta.

Bugu da kari majiyar ta tabbatar da cewa, soyayyar Sarkin Kano Aminu Ado da Hajiyayye ba sabuwa bace, domin kuwa sun dade suna soyayya, tun kafin ma ya zama Sarkin Kano.

An haifi Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a shekarar 1961. Inda ya zama Sarki na 15, a cikin jerin sarakunan Fulani da akayi a jihar Kano.

Gwamnan Kano mai ci a yanzu wato Abdullahi Umar Ganduje, shine ya nada Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano, a ranar 9 ga watan Mayu, shekarar 2020.

Leave a Comment