An zabi yar jihar Kano, a matsayin wadda tafi duk matan Najeriya kyau.

Yar jihar Kano mai suna Shatu Garko ta zama gwarzuwa, inda ta lashe gasar wadda tafi kowa kyau a gaba daya ilahirin matan Najeriya.

Shatu Garko dai ta samu wannan matsayi ne na lashe gasar sarauniyar khau ta Najeriya, bayan da ta doke kyawawan mata abokan gwabzawar ta ta har su 18.

Kuma an gudanar da bikin tantancewar ne a ranar Juma’a da daddare, a Landmark Center dake garin Legas Najeriya. Inda a Turance ake kiran gasar “Miss Nigeria.”

Shatu Garko ta kasance ‘yar asalin jihar Kano ce, inda a yanzu takeda shekaru 18 da haihuwa.

Kuma wannan gasa da aka gabatar itace karo na 44, inda a tarihin gasar, wannan ne karo na farko da mace mai Hijabi ta lashe ta.

Wadda tazo ta biyu a gasar itace Nicole Ikot, sai kuma Kasarachi Okoro da ta zo ta uku.

Shatu Garko dai ta karɓe kambun ne daga hannun Etsanyi Tukura wadda ta kasance ‘yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43, wato kafin wannan gasar da akayi.

Wato gasar da yar jihar Taraba tazo ta daya, anyi ta ne a shekarar 2019.

A cewar masu shirya gasar, wadda ta yi nasara zuwa ta daya, za ta samu kyautar makuden kuɗade har naira miliyan 10, sannan zata zauna a gidan alfarma na tsawon shekara ɗaya, haka zalika zata samu kyautar dalleliyar mota, sannan kuma daga karshe zata zama jakadiya ta musamman ga wasu kamfanoni.

A takaice dai zamu iya cewa duk wadda tayi nasarar zuwa ta daya a wannan gasa, to kawai sai dai ayi mata sam barka.

Kusan dai zamu iya cewa wannan wani sabon al’amari ne, wato aga mace Bahaushiya ta shiga gasar kyau, ba kasafai hakan ta fiye faruwa ba. Wato dai abun yafi karfi ne a ‘bangaren Turawa da fararen fata.

Sai a Najeriyar ma anayi, amma kuma abin yafi karfi a bangaren Kudancin kasar.

To yanzu dai suma Hausawa sunce baza’a barsu a baya ba, inda suma suka fara fitowa suna shiga cikin irin wadannan gasa.

Shatu Garko tayi godiya ta musamman ga wadanda suka shirya wannan gasa da kuma wadanda suka dauki nauyi, inda ta wallafa godiyar akan shafin ta na Instagram.

Daga karshe kuma tayi godiya ga al’umma abisa nuna goyon bayan su, da kuma soyayyar su a gare ta.

Yanzu kuma ga kadan daga cikin hotunan Shatu Garko wato wadda tafi kowa kyau a cikin matan Najeriya.

Leave a Comment