Nafisa Abdullahi ta shiga gaban duk jaruman Kannywood a matakin duniya.

Nafisa Abdullahi ta samu wani gagarumin ci gaba, wanda har abada bazata taba mantawa da shi ba a rayuwar ta.

Nafisa Abdullahi wadda akafi sani da Sumayya a cikin shiri mai dogon na Kamfanin Saira Movies wato Labari na, wanda ake haskawa a tashar Talabijin ta Arewa24, ta shiga jerin mutane 10 a duniya da akafi neman karin bayani akansu, a manjajar Matambayi Baya Bata, wadda ake kira “Google” a Turance.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta shiga jerin ne, tare da taurarin fim din kudancin Najeriya da ake kira Nollywood, irin su Destiny Etiko, Tonto Dikeh da Zubby Michael.

Sai dai manhajar Google din sun saka sunan Nafisa Abdullahi a cikin jerin jaruman Kudancin Najeriya na Nollywood, maimakon a ganta a bangaren Kannywood.

A lissafin matan Kannywood da sukafi shahara Nafisa Abdullahi ce ta farko, sai Rahama Sadau wadda take take mata baya, sannan sai Fati Washa, daga nan kuma sai Maryam Yahaya, sai kuma ta karshe, wato jaruma Hadiza Gabon.

Leave a Comment