An kama matashin da yake zina da ‘yan mata da sunan zai saka su a fim.

Yan sanda sun kama wani matashi, wanda yake yaudarar yan mata yayi zina dasu kuma ya karbi kudin su, da sunan cewa zai saka su a fim.

Wani matashi mai suna Abdullahi Sa’idu wanda yai kaurin suna wajen yin amfani da sunan wasu daga cikin jaruman masana’antar Kannywood domin ya damfari mutane. A halin yanzu dai wannan matashi ya shiga hannun jami’an tsaro.

Dan damfarar yana amfani ne sunan wani fitaccen mai shirya fina-fina a masana’antar ta Kannywood a wato Abubakar Bashir Maishadda. Inda ya bude shafin Facebook da sunan Maishaddan domin ‘dana tarko ga masu sha’awar shiga harkar ta fina-finai.

Tabbas a wannan lokacin dai zamu iya cewa a kaf ilahirin masu shirya fina-fina a masana’antar Kannywood, babu wanda ya kai Maishadda yawan fitar da fina-finai, a karkashin kamfanin sa na “Maishadda Global Resources.” Wanda kuma wata kila shine yasa wannan macucin matashi yayi amfani da sunan sa.

Inda shi kuma Maishadda ya kasance yaron Ali Nuhu ne, shiyasa duk inda kaga Ali Nuhu, to zaka Maishadda.

wannan da kuke gani a kasa, shine hoton Abubakar Bashir Maishadda, domin wanda bai sanshi ba ya sanshi.

Sai kuma hoton wannan matashi wato Abdullahi Sa’idu, wanda ya samu sana’a ta damfarar ‘yan mata da yaudara su Kuma da sunan Maishaddan.

Maishadda shine da kansa ya wallafa wannan al’amari akan shafin sadarwar sa na Instagram, inda dan damfarar da bakin sa yake bayyana wa duniya irin damarun da yake amfani da su, wajen janyo hankalin mutane, da kuma yanda yake cutar su. Kuma a bisa la’akari da kalaman matashin, mata sune sukafi fadawa tarkon sa.

To Maishadda dai ya wallafa wannan faifan bidiyo, inda ya gargadi mutane da su kula, kuma su kiyaye.

Mafi akasari mata sune sukafi fadawa cikin irin wannan tarko na wadannan mayaudara, domin kuwa mata sunfi maza bayyana sha’awar su a fili a cikin wannan harka ta fina-finai fiye da maza.

Idan mat suna neman shiga masana’antar Kannywood idanun su sai su rufe, duk wanda suka fuskanci zai taimake su, sai su saki jiki gaba ‘daya, shi kuma daga nan shikenan ya samu damar da zai iya yin duk abinda yaga dama dasu.

A irin wannan al’amari wasu matan sai a dinga yin amfani dasu wato (zina) da sunan cewa za’a saka su a fim. Wasu kuma ayi ta yaudarar su ana karbar kudin su, inda kuma za’ai tayi musu roman baka da cewa ai za’a hadasu da manyan jarumai a cikin fim.

Hakika zamu iya cewa wannan lamari ba sabo bane, wato yanda wasu bata gari suke amfani da sunan jarumai ko masu bada umarci ko masu shirya fina-finai suna damfarar mutane kudi. Wanda kuma bincike ya tabbatar da cewa irin wannan damfarar tafi ‘karfi akan mata.

Kuma irin wannan abu yana faruwa a duk duniya, inda bata gari suke amfani da sunayen fitattun mutane wajen damfara da yaudara da cuta.

To daga karshe muma daga nan shafin Mujallar Hausa, muna kira ga mutane musamman mata da suyi taka tsan-tsan su dinga kulawa, domin a irin haka ma wata zata iya rasa ranta gaba daya.

Sannan kuma mata ku sani cewa shi mugu bashida kama, karku bari dadin baki ya dinga tasiri akan ku.

Duk wadda take son shiga fim akwai hukumomi da zataje tayi rijista da su. Idan kuma taje yin rijistar, a nan ne za’a gaya mata dukkan abubuwan da ake bukata daga gurin ta. Wannan dai itace kadai ingantacciyar hanya da ake
shiga masana’antar Kannywood.

Muna fata Allah Ya shiga tsakanin na gari da mugu, domin babu ‘karfi, babu dabara sai a gurin Sa.

A daidai nan kuma zamu saka muku faifan bidiyon wannan matashi, domin kuji daga bakin sa, inda ya bayyana yanda yake aikata wannan aika-aika.

Kuci gaba da kasancewa da shafin Mujallar Hausa, domin samun labarai daga kowanne fanni. Mun gode.

Leave a Comment