Bidiyo. Mahaifin yarinyar da aka kashe ya fashe da kuka akan abinda akai wa yar sa.

Allahu Akbar. Har yanzu dai a jihar Kano ana cikin alhini na abin al’ajabin da ya faru, na yin garkuwa da karamar yarinyar nan yar shekara 5.

Cikin alhini da zubar da hawaye mahaifin yarinyar tare da ‘yar uwar mahaifiyar ta sun yi magana da manema labarai, akan yanayin da suka tsinci kan su bayan faruwar al’amarin.

Mun samu labari daga majiyoyi da dama akan rayuwar mutumin da yai garkuwa da yarinyar ya kuma kashe ta. Inda muka samu cewa a zahiri mutumin kirki ne, kuma baya wasa da Addini, shiyasa wasu suke al’ajabin wannan abu da ya aikata.

Domin wasu ma sun fada cewa idan aka gaya musu zai iya aikata haka, bazasu yarda ba, domin a zahiri yanayin sa ko kadan bai nuna haka ba.

To a halin yanzu dai kowa yana zuba ido, domin ganin irin hukuncin da za’a yanke wa wannan mutum, tare da duk wadanda suka taya shi wajen aiwatar da aikin.

Yanzu kuma zamu saka muku faifan bidiyon, inda zakuga bayanin mahaifin yarinyar, da kuma bayanin wasu daga cikin iyayen ta mata.

Ga bidiyon nan a kasa.

1 thought on “Bidiyo. Mahaifin yarinyar da aka kashe ya fashe da kuka akan abinda akai wa yar sa.”

Leave a Comment