Wata jarumar Kannywood ta yanke hukuncin ficewa daga masana’antar.

Matashiyar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Husna Adam Annuri, ta ayyana ficewar ta daga masana’antar.

Sai dai jarumar bata bayyana makasudi, ko kuma dalilin fitar tata ba, kawai dai ta bar abun a cikin ‘kokon zuciyar ta, duk da cewa ta san mutane zasu so su san dalilin ficewar da tayi.

To zamu iya cewa dai jaruma Husna ba itace farkon wadda ta ‘dauki wannan mataki ba, wato kafin ita akwai wasu jaruman da suka aikata irin wannan hukunci da ta zaba wa
kan ta.

Sai dai kuma duk jaruman da suka fice, basa fadar dalili ficewar, inda kawai suke barin mutane a cikin shaci fadi.

To ita dai Husna ta wallafa wannan magana ne akan shafin sadarwar ta na Instagram, inda tai rubutu kamar haka “Assalamu Alaikum Warahmatullah, Ni Husnah Adam Annuri daga yau 21st January 2022, na bar masana’antar film in Sha Allah”.

Sai dai bayan jarumar tayi wannan wallafa, sai sauran jarumai sukai ta tura mata sakon taya murna, inda kowa yake mata murnar wannan zabi da tai wa kan ta.

To abin tambayar anan shine mai yasa sauran jarumai har da mata, suke mata murna akan hukuncin da ta yanke na fita daga masana’antar ta Kannywood, alhalin su kuma suna ci gaba da kasancewa a ciki?

To ga dai hoton da jaruma Husna ta wallafa kamar yanda muka ‘dakko daga kan shafin na su na Instagram.

2 thoughts on “Wata jarumar Kannywood ta yanke hukuncin ficewa daga masana’antar.”

Leave a Comment