Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai sayar da kamfanonin kasar har guda 42.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki aniyar siyar da wasu kamfanoni mallakin kasar har guda 42 mallakin Gwamnati.

Hukumar sayar sa kadarorin kasar wato NCP, wadda mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ke jagoranta, itace ta bada umarni ga hukumar kula kamfanonin gwamnati wato BPE, dangane da batun cefanar da kamfanonin.

A halin yanzu dai gwamnati zata siyar da kamfanoni guda goma sha daya (11) wadanda suke a bangaren makamashi, da kamfanoni goma (10) a bangaren masana’antu da ayyuka. Sai kuma kamfanoni takwas (8) na bangaren noma da albarkatun kasa, daga karshe kuma sai kamfanoni goma sha (13), su kuma na bangaren abubuwan more rayuwa da hadakar gwamnati da yan kasuwa, kamar yanda BPE ta fitar da sanarwa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Hukumar BPE ta fitar da wannan sanarwa ne bayan wata tattaunawa da tayi a fadar shugaban kasa da hukumar da ke da alhakin siyar da kadarorin gwamnatin kasar, inda nan da nan hukumar ta amince da kudurin BPE na aiwatar da aikin.

Leave a Comment