Bidiyo. “Ba a cikin fim jarumai suke samun makuden kudi ba”. Inji Rukayya Dawayya.

Jarumar Kannywood Rukayya Dawayya ta bayyana cewa jaruman fim, ba wai a cikin fim din suke samun makuden kudade ba. Inda tace suna samun kudin ne a wajen tallika na kamfanoni.

Jarumar tayi wannan magana ne a lokacin da ake cecekucen zancen Ladin Cima, inda ta wallafa akan shafi ta na sadarwa.

Hakika shi dama fim, ba shine yake sa jarumi ko jaruma su zama hamshakan masu kudi ba kamar yanda Rukayya ta fada. Shi dai fim shine zai baka daukaka, daga nan sai ita kuma daukakar ta zama silar samun kudi masu yawan gaske.

Yanzu dai ga wani dan gajeren bidiyo. Wanda Rukayya Dawayya take wannan bayanin.

1 thought on “Bidiyo. “Ba a cikin fim jarumai suke samun makuden kudi ba”. Inji Rukayya Dawayya.”

Leave a Comment