Abinda yasa tallace-tallacen yaya mata yake kara yawaita a Arewacin Najeriya.

Da yawan ƴanmatan karkara yanzu wasun su sun ta’allaka ne wurin maida hankali akan tallah, haka ma wasu daga mutanen gari suna tallar. Kuma mafi yawanci ƴan mata ne.

Da farko dai ya kamata a duba menene amfanin wannan tallan da suke yi? sannan kuma daga baya a duba rashin amfanin sa.

A iya dogon nazari da tunanina na gano dalilai guda biyu da yasa ƴaƴa mata suke tallah.

Dalilan sune:

1) Talauci
2)Maraici

Bari mu ɗauki dalili na farko wato Talauci:

Talauci yana jefa mutum cikin mawuyacin hali, wanda idan mutum bai yi imani ba zai iya kauce hanya, wanda yayi imani kuma zai shiga neman na kansa ne ba dare ba rana, ko da a cikin neman nasa zai rasa wani abu mai muhimmanci. Idan ya zamana talauci yayi wa uwa da uba yawa to fa karkayi mamaki don sunje sun ciwo bashin gyaɗa sun ɗorawa ƴar su ta tafi kasuwa ta siyar ta dawo an ɗauki riba an biya bashi, talauci zai iya saka ƴa da kanta ta fita nema, acan zata iya samun uwar gida wadda zatace ta rinƙa zuwa tana ɗora mata tallah suna raba riba, kuma ita da iyayen ta zasu amince da hakan, saboda su dama suna neman yadda zasu yi ne, don haka zasu dauki abin a matsayin mafita.

Sai kuma dalili na biyu, wanda shine maraici kamar yanda muka ambata a sama.

2) Maraici: Duk marayan da bashi da mataimaki tabbas rayuwar sa tana cikin wani hali, wani lokacin tallah na kasancewa akan marayun da iyayensu maza suka mutu, mahaifiyar su ce zata ɗora masu tallan da kanta, saboda su samu abin sarrafawa domin su rayu.

A taƙaice amfanin tallah shine: Yana hana mutuwar zuciya domin neman na kansu suke. Sannan kuma gara yarinya ta fita tallah akan ta fita ta ɗauki kayan wani a matsayin sata.

Rashin amfanin tallah.

1) Tallah na hana zuwa makaranta domin babu lokaci.

2) Yana kuma lalata tarbiyyar yara domin bakasan dawa suke mu’amala ba.

Kira na ga iyayen ƴaƴa wanda suka dogara da tallah shine: Idan har lallai ya zama dole sai kin ɗorawa ɗiyar ki tallah saboda yanayin rayuwa, to ki duba abubuwa guda biyu:

1) lokaci: dole ne ki saka lokacin da zata riƙa fita da dawowa, kuma a cikin lokutan a ware na zuwa makarantar Boko da Islamiyya. Amma idan har ɗiyar ki zata fita tun safe sai dare ta dawo sannan kuma ta dawo miki da kuɗin da suka linka na abin da kika kasa mata, to wallahi hakan ba zai haifar miki da Ɗa mai ido ba.

2) Tarbiyya: Ki lura da wanda take mu’amala, ina take kai tallar? wurin ya dace ƴa mace taje ko kuwa? Idan zata bar gida wace irin shiga take yi? Mai take fita da shi kuma dame take dawowa?.

Dole iyaye sai kunsa ido akan irin wadannan abubuwan, sannan ya kamata ace masu ruwa da tsaki sunyi wani tsari akan tallar ita kanta, tare da dokoki, wandanda zasu sa a tsabtace harkar, idan har ta zama dole sai an yi ta.

Allah yasa mu dace.

Leave a Comment