An daura auren Aisha Tsamiya a cikin sirri.

Aisha Tsamiya ta shammaci mutane, inda aka daura auren ta a cikin sirri. Babu gayyata, babu shagalin biki, babu kuma sanarwa.

Aisha Aliyu Tsamiya dai tayi wani abu wanda yai matukar daure wa mutane kai, domin kuwa da kanta ta bada sanarwar cewa auren ta sai watan gobe, alhalin kuma ta san cewa hakan ba gaskiya bane.

Mutane da dama sun shiga rudani akan wannan aure. Inda ake tunanin akwai wani babban dalili da yasa jarumar ta aikata haka, wanda ita kadai ta barwa kan ta sani.

Domin kuwa har yan uwan sana’ar ta wato jaruman Kannywood, Amarya Aisha bata gayyace mafi yawa daga cikin su ba.

Aminin mahaifin jarumar mai suna Alhaji Idris Haruna Tsamiya Babba, shine ya tabbatar da cewa tabbas an daura auren, sai dai yace shima bai samu halartar daurin auren ba saboda canja lokacin daurin auren da akayi.

Alhaji Haruna ya bayyana haka ne ta wayar tarho, a lokacin da tashar YouTube ta tsakar gida suka tuntube sa.

Bari kuma kuji yanda tattaunawar ta kasance.

3 thoughts on “An daura auren Aisha Tsamiya a cikin sirri.”

Leave a Comment