Adam A. Zango ya gwangwaje abokin sa da kyautar dalleliyar mota.

Abota mai dadi, jarumin Kannywood Adam A Zango yayi wata bajinta, inda yai wa babban abokin sa mai suna Kochila kyautar mota kerar Honda.

Duk wanda ya san Adam A Zango, to tabbas ya san shi da Kochila domin kuwa sun dade tare a cikin fadi tashi da fafutuka a masana’antar Kannywood. Kawai dai Allah ne Ya daga darajar Adamun sama da ta Kochila.

Sai dai tun a baya an san jarumin da shakikan abokan sa, irin su Falalu A. Dorayi da Tahir I. Tahir. Wanda a shekarun baya suka taba samun sabani, harma Adamun ya fito yake bada sanarwa cewa har abada babu shi babu abota da kowa.

Yanzu dai bari kuga hoton wannan mota son kowa kin wanda ya rasa, da jarumin ya ba wa abokin nasa.

1 thought on “Adam A. Zango ya gwangwaje abokin sa da kyautar dalleliyar mota.”

Leave a Comment