Rahma Sadau tayi zafafan maganganu akan ta’addancin da akai a jirgin kasar hanyar Kaduna.

Jaruma Rahma Sadau ta fusata, kuma ta fadi abinda ke cikin zuciyar ta akan ibtila’in da ya faru a hanyar Kaduna zuwa Abuja, na jirgin kasar da Yan Bindiga suka tare, suka kashe na kashewa suka kuma tafi da wasu.

Hakika wannan al’amari ya tada hankulan mutane, musamman yan Arewacin Najeriya. Domin kuwa jama’a da dama sun nuna bacin ransu akan lamarin.

Jaruman Kannywood da dama sun aika zafafan sakonni zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran mahukunta, inda suke cewa Buhari da Gwamnatin sa sun gaza a fannin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, da ma sauran abubuwa da dama.

Daga cikin jaruman, Rahma Sadau tayi zafafan kalamai na jin haushi da bacin rai, inda take aika sakon ta kai tsaye ga ilahirin yan kasar ta Najeriya.

Kasancewar a jiya anyi wasan kwallon kafa, tsakanin kasar Ghana da kasar Najeriya, inda akai wasan a babban birnin tarayya Abuja. Kuma an wadata filin wasan da jami’an tsaro, shiyasa Rahma ta alakanta maganar ta batun wasan kwallon kafar.

Jarumar dai ta wallafa zafafan maganganun nata ne a cikin harshen Turanci, wanda a takaice zamu fassara abinda ta fada a harshen Hausa.

Rahman ta fara ne da cewa “A yau, bisa la’akari da jami’an tsaron da aka zuba a filin wasan kwallon kafa na Abiola, na fahimci cewa Nigeria tanada karfin magance matsalar tsaro, amma kawai sun zabi su banzatar da kashe rayukan al’umma. Allah wadaran jami’an tsaron kasar”.

Taci gaba da cewa “Mu yan Arewa, mu muka kawo wannan da kan mu, mun zabi aci gaba da kaskantar damu saboda muna jin tsoro. Amma kuma mun kasa fahimtar cewa karfin fa a hannun mu yake, bama so muce shugabannin mu sun gaza, alhalin tabbas sun gaza din. Bazaka san zafin ciwo ba, sai kaji rauni a jikin ka”.

“Allah  ne Ya kiyaye hadarin bai ritsa mu ni da yar uwata ba, saboda mun so hawa jirgin a ranar, sai bamu samu ba. Amma kuma duk da haka munada abokai da yan uwa a cikin wannan jirgi. Don Allah yaushe wannan al’amarin bakin cikin zai kare”.? Rahma tayi tambaya.

Daga karshe sai jarumar tace “Abun ma yana kara ta’azzara idan zabe ya karato, kuma koda yaushe manufar su itace rusa Arewa. Abinda zance kawai shine, kowa ya mallaki katin zaben sa, sannan kayi taka tsantsan akan wanda zaka zaba. Amma kuma suwa zaka zaba? Irin wadannan mutanen da suka shugabantar mu yanzu?. Kawai dai don Allah kowa ya mallaki katin zaben sa”.

Yanzu kuma ga hotunan rubutun da jarumar ta wallafa.

2 thoughts on “Rahma Sadau tayi zafafan maganganu akan ta’addancin da akai a jirgin kasar hanyar Kaduna.”

  1. I was extremely pleased to discover this page. I want to to thank you for ones time due to this wonderful read!! I definitely appreciated every part of it and I have you bookmarked to look at new information on your web site.

    Reply

Leave a Comment