Bidiyo. An daura auren Nafisa Ishak, jarumar da ta zagi Shek Daurawa.

Jarumar Kannywood Nafisa Ishak wadda ta yi wa Shek Daurawa mummunan martani, ta shiga daga ciki domin kuwa tuni wani bawan Allah yayi Wuf da ita.

Jarumar ta wallafa batun auren akan shafukan ta na sadarwa, sai dai bayan tayi wallafar, sai kuma ta goge duk wata wallafa da tayi akan shafin ta na Tiktok, inda tabar wallafar auren kadai akan shafin. Amma kuma bata goge wallafofin shafin ta na Instagram ba.

Nafisa Ishak tayi wata magana da ta dauki hankalin mutane, inda ta nuna cewa abinda ya faru tsakanin ta da Shek Daurawa ya zame mata alkhairi, wanda in shaa Allah zamu kawo muku hotunan wallafofin da jarumar tayi.

Kafin ma mu nuna wallafar jarumar, zamu iya cewa tabbas ta wata fuskar abinda ya faru tsakanin ta da Malam Daurawa ya zama alkhairi a rayuwar ta, domin kuwa yawancin mutane ma basu santa ba, sai bayan ta zagi malamin.

A cikin wallafar, jarumar tayi magana kamar haka “Kalubalen rayuwa yana tafe ne hadi da nasarar rayuwa, idan kayi hakuri da kalubalen ka, sai ya zama nasarar rayuwar ka amma fa sai anyi hakuri. Alhamdu Lillah ni dai kalubalen rayuwa ta ya zama nasara a gare ni. Alhamdu Lillah Alhamdu Lillah, Allah Kasa sai mutuwa ce zata raba mu mai tausayi na”

Sai kuma wallafar da jarumar tayi wadda ta nuna yanda zatai kewar abokan ta, inda tace “Missing you all my friends, Allah Ya ba wa kowa”

To Allah dai ya bada zaman lafiya, ga kuma wani gajeran faifan bidiyo wanda amaryar take cashewa da angon na ta.

2 thoughts on “Bidiyo. An daura auren Nafisa Ishak, jarumar da ta zagi Shek Daurawa.”

  1. I was extremely pleased to discover this page. I want to to thank you for ones time due to this wonderful read!! I definitely appreciated every part of it and I have you bookmarked to look at new information on your web site.

    Reply

Leave a Comment