An dakatar da Shek Nuru Khalid daga limanci akan sukar Gwamnati.

Babban malamin Addini Shek Nuru Khalid wanda ake wa lakabi da Dijital Imam ya hadu da fushin gwamnatin Buhari, inda aka dakatar dashi daga limancin masallacin da ya ke jagoranta a Abuja.

Shek Khalid dai malami ne wanda yai kaurin suna wajen aika wa gwamnati zafafan sakonni, musamman idan yaga anyi wani abin da bai dace ba.

Mafi akasari malamin yafi yin magana akan matsalar tsaro, da ta addabi Najeriya, wanda idan baku manta ba ma a juma’ar data gabata malamin yayi wasu zafafan maganganu akan harin jirgin kasar da yan ta’adda suka kai a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kuma maganar da malamin yayi a yayin Hudubar Juma’ar itace ta janyo wannan dakatarwa da akai masa.

A lokacin Hudubar, malamin yayi maganganu da dama, daga ciki ya ja hankalin talakawan kasar ta Najeriya akan cewa idan zabe yazo kar wanda ya fito yayi, har sai an daina kashe rayuka tukunna.

Kwamitin kula masallacin rukunin gidajen yan majalisu, wanda yake a unguwar Apo a babban birnin tarayya Abuja, shine ya dakatar da malamin. Kuma anyi dakatarwar ne sakamakon Hudubar da yai a ranar Juma’ar da ta gabata.

Daga karshe ga Hudubar da Malamin yayi, wadda ta janyo aka kore shi daga limancin.

2 thoughts on “An dakatar da Shek Nuru Khalid daga limanci akan sukar Gwamnati.”

  1. I was extremely pleased to discover this page. I want to to thank you for ones time due to this wonderful read!! I definitely appreciated every part of it and I have you bookmarked to look at new information on your web site.

    Reply

Leave a Comment