Za’a dakko sojojin haya a Arewacin Najeriya domin magance matsalar tsaro a kasar.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa’i tare da sauran gwamnonin Arewacin Najeriya, suna shirin yin hayar sojoji daga kasashen waje domin magance tashin hankalin rashin tsaro da yaki ci yaki cinyewa.

Kuma gwamnanin sun bada sharadin cewa, zasu aiwatar da wannan aiki matukar Gwamnatin Muhammadu Buhari bata dauki matakin da ya dace ba.

Bayan gwamnan Kadunan yaje har fadar shugaban kasa ya gana da shi, akan harin jirgin kasar da aka kai a jihar sa, har aka kashe  mutane, aka raunata wasu, aka kuma sace wasu, wanda har yanzu ba’a gama tantance mutanen da aka sace ba. Gwamnan ya shaida wa manema labarai cewa ba kowa ne ya kai wannan hari na jirgin kasa ba, sai yan Boko Haram.

Sai dai gwamnan yace, a lokacin tattaunawar su da shugaban kasa, Buharin ya tabbatar masa da cewa Gwamnatin sa zata dauki kwakkwaran mataki nan da wasu yan watanni masu zuwa.

1 thought on “Za’a dakko sojojin haya a Arewacin Najeriya domin magance matsalar tsaro a kasar.”

  1. I was extremely pleased to discover this page. I want to to thank you for ones time due to this wonderful read!! I definitely appreciated every part of it and I have you bookmarked to look at new information on your web site.

    Reply

Leave a Comment