Bidiyo. Jami’an tsaro ne suke ba wa yan ta’adda bindigogi a Arewacin Najeriya. Inji Shek Ahmad Gumi.

Fitaccen malamin Addini, Shek Ahmad Gumi, ya fallasa wata magana mai matukar mahimmanci, inda yake tabbatar da cewa jami’an da ake biyan su domin su kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sune da kansu suke ba wa yan ta’adda bindigogin da suke ta’addanci dasu.

Oh! Duniya ina zaki damu? Lamarin Najeriya dai ya gama tabarbarewa da hargitsewa, ana yin wasu abubuwa a kasar, tamkar babu shugabanni masu tsawatarwa.

To amma kuma ta bakin malam Bahaushe da yake cewa “Mai dokar bacci ya bige da gyangyadi” domin kuwa su kansu masu dokar sune suke fara ragargaza ta.

Mafi akasari idan kaga anyi aiki da doka akan mutum, to da wuya kaga ba talaka bane, domin shine idan ya kuskure ya karya doka, sai ayi masa hukunci daidai da abinda ya aikata, ko ma sama da abinda ya aikata.

To yanzu dai bari kuji yanda Shek Gumi ya fasa kwai mai tsananin wari, akan kasar ta Najeriya. Ga labarin nan a kasa kamar yanda muka samu daga tashar Kundin Shahara.

1 thought on “Bidiyo. Jami’an tsaro ne suke ba wa yan ta’adda bindigogi a Arewacin Najeriya. Inji Shek Ahmad Gumi.”

  1. I was extremely pleased to discover this page. I want to to thank you for ones time due to this wonderful read!! I definitely appreciated every part of it and I have you bookmarked to look at new information on your web site.

    Reply

Leave a Comment