Bidiyo. Rigimar Shek Nuru Khalid da Gwamnatin Buhari ta canja salo.

A wannan lokacin dai babu zancen da yake yamutsa hazo a Arewacin Najeriya, kamar maganar korar da Gwamnatin kasar tai wa babban malami Shek Muhammad Nuru Khalid.

Kamar yanda kuka sani, korar dai ta biyo bayan wata magana da malamin yayi a yayin da yake gabatar da Huduba a ranar Juma’ar da ta gabata.

Inda Shek yai magana akan yanda yan ta’adda suke sha’anin su, wato suke cin karen su ba babbaka a Najeriya, musamman kuma bangaren Arewaci, inda Malamin ya aika wa Gwamnatin zazzafan sako akan harin jirgin kasar da wasu yan bindiga suka kai, a lokacin da jirgin yake tafiya dauke tulin fasinjoji akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, wanda rahotanni suka tabbatar da cewa an kashe mutane da dama a harin, sannan kuma an tafi da wasu, wadanda har yanzu ba’a gama tantance adadin su ba.

Hakika yawancin yan Najeriya sunyi Allah wadai da korar malamin daga limancin, inda mutane suke ganin wannan ba komai bane face tsantsar zalunci da kuma tauye hakki.

Kafin muci gaba, bari kuji rahoton hasalar da wasu yan kasar ta Najeriya suka yi akan al’amarin.

To daga bisani kuma mun samu wani labarin wanda shafin BBC Hausa suka tattauna ta wayar tarho tare da Sanata Dansadau, wanda ya bayyana makasudin abinda yasa suka kori malamin daga limanci. Shima kafin mu dora, ga rahoton nan a kasa.

Shek Nuru Khalid yace zai iya janye kalaman sa, idan Gwamnatin ta biyo ta hanyar da ta dace, amma ba irin wannan hanyar ba. Inda malamin ya bayyana haka a hirar da Jarida Radio.

Ku duba rahoton a kasa.

Daga karshe Malam ya sake bayyanawa a hirar kafa da kafa, da BBC Hausa sukai dashi, wanda a cikin wannan tattaunawar, malam cikin fushi ya fada cewa, Da ya daina fadar gaskiya, gwara ma ya koma sana’ar Dako.

Hakika Shek Khalid ya bayyana asalin abinda ke cikin zuciyar sa, akan kasar Najeriya da shugabannin ta. Ga cikakkiyar hirar a kasa.

1 thought on “Bidiyo. Rigimar Shek Nuru Khalid da Gwamnatin Buhari ta canja salo.”

  1. I was extremely pleased to discover this page. I want to to thank you for ones time due to this wonderful read!! I definitely appreciated every part of it and I have you bookmarked to look at new information on your web site.

    Reply

Leave a Comment