Bidiyo: Professor Maqari bai goyi bayan Shek Nuru Khalid ba akan maganar kin yin zabe.

Babban malami, kuma limamin masallacin “Central Mosque” dake birnin tarayya Abuja. Wato Professor Maqari, yayi tsokaci mai matukar mahimmanci akan maganar Shek Nuru Khalid, wadda yake cewa Yan Nigeria kar su fito zabe, har sai Gwamnati ta samar da tsaro tukunna.

Wanda kuma Nuru Khalid yayi maganar ne duba da halin da ake ciki na kashe-kashen rayuwaka a Arewacin Nigeria ba gaira babu dalili.

Sannan kuma babban abinda ya tunzura malamin har yace kar wanda ya fito zabe, shine abinda ya faru na kwanan nan, wato batun jirgin kasar da Yan Ta’adda suka kai hari suka tayar da Nakiya, suka bude wuta da harbe-harbe, suka kashe na kashewa suka kuma yi awon gaba da wasu. Inda wannan mummunan al’amari ya faru a lokacin da jirgin yake tafiya akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

To lallai Shek Maqari yayi wata magana mai mahimmanci akan wannan lamari, inda ya tabbatar da cewa ko munyi zabe ko bamuyi zabe ba, sai an rantsar da shugaban kasa da gwamnoni da yan majalisu da sauran su. Don haka ko bamu zaba ba sai wasu sun zaba mana.

Inda Maqari yace babbar mafita itace, idan kana ganin wani shugaba yana maka zalunci, to ka fito ranar zabe kayi amfani da kuri’ar ka, ka tsige shi. Idan kuma kana ganin akwai wani adali wanda yake neman takara, to kaje ka zabe shi.

Bari dai mu saka muku bidiyon bayanin malamin, domin kuji yanda yai maganar daka bakin sa.

2 thoughts on “Bidiyo: Professor Maqari bai goyi bayan Shek Nuru Khalid ba akan maganar kin yin zabe.”

  1. I was extremely pleased to discover this page. I want to to thank you for ones time due to this wonderful read!! I definitely appreciated every part of it and I have you bookmarked to look at new information on your web site.

    Reply

Leave a Comment