Bidiyo. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, Muneerat Abdussalam Ta Gamu Da Aljanu A Zahiri.

Fitacciyar mai jan magana a shafin YouTube, wato Muneerat Abdussalam, ta gamu da bakaken aljanu a cikin bacci, wanda kuma bayan ta farka ya zama zahiri, kamar yanda ta bada labari.

Abin mamaki, abin dariya kuma abin al’ajabi. Muneerat ta bada labarin yanda tai arangama da Aljanu a cikin mafarki, wanda tace har fada da kokawa tayi da mutanen boyen.

Abin kuma da ya bada matukar mamaki shine, yanda aljanun suka ji mata ciwo a cikin fadan, bayan kuma ta farka sai taga tabon ciwon da suka ji mata. Lamarin da ita kanta yayi matukar bata mamaki.

A cewar ta, wasu ne suke kokarin ganin bayan ta shiyasa suka tura mata Aljanu, inda tayi alwashin cewa tafi karfin su.

To wasu daga mutane dai suna fassara wannan al’amari da shan kwaya, wato suna ganin cewa wannan ba komai bane face aikin shaye-shaye.

Muneerat dai tayi kaurin suna ta fannin dakko magana, inda take maganganu akan tsaraici akan shafin YouTube, wadanda suka saba da tarbiyyar Addinin Musulunci, sai dai ita tana yin hakan ne da sunan sayar da magungunan maza da mata.

Yanzu kuma ba tare da bata lokaci ba, bari kuji labarin dambarwar da aka sha, tsakanin Muneerat da Aljanu, kamar yanda take fada da bakin ta. Ga bidiyon nan a kasa.

1 thought on “Bidiyo. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, Muneerat Abdussalam Ta Gamu Da Aljanu A Zahiri.”

Leave a Comment