Bidiyo: Shek Nuru Khalid shine jagora kuma shugaban yan ta’adda a Najeriya. Inji wani malami.

Ana wata ga wata. Wani malami ya kawo wata sabuwar magana, wadda ta saba da fahimtar yawancin yan Najeriya, Inda malamin yake fada cewa Shek Nuru Khalid shine jagoran yan ta’adda a Arewacin Najeriya. Hakika mutane sunyi mamakin wannan magana da malamin yayi, domin kuwa kusan kowa yana kallon Shek Khalid a matsayin wani mutum … Read more

Bidiyo. Jami’an tsaro ne suke ba wa yan ta’adda bindigogi a Arewacin Najeriya. Inji Shek Ahmad Gumi.

Fitaccen malamin Addini, Shek Ahmad Gumi, ya fallasa wata magana mai matukar mahimmanci, inda yake tabbatar da cewa jami’an da ake biyan su domin su kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sune da kansu suke ba wa yan ta’adda bindigogin da suke ta’addanci dasu. Oh! Duniya ina zaki damu? Lamarin Najeriya dai ya gama tabarbarewa da … Read more

Bidiyo. Manyan malamai sun zubar da ruwan hujjoji akan maganar jaruma Nafisa Ishak.

Wasu daga cikin manyan malaman Addini sunyi yayyafin hujjoji dangane da maganar da ta ja cecekuce, batun batun Shek Daurawa, da kuma martanin da jarumar Kannywood mai suna Nafisa Ishak ta mayar wa malamin. To da farko dai jama’ar gari ne suka fara tsoma baki akan wannan magana, inda wasu suke ganin Malamin baiyi daidai … Read more

Bidiyo. Ingantacciyar magana akan gwajin cuta kafin aure – Bini Usman.

Hukuncin gwajin cuta kafin aure. Shek Muhammad Bini Usman ya fede biri har wutsiya akan wannan al’amari da yake shige wa mutane duhu. Hakika wannan wata babbar magana ce wadda take bukatar wayar da kan al’umma akai, domin akwai abubuwan da ake aikatawa wadanda ko kadan basu dace ba. Da farko dai zamu iya cewa … Read more

Wata sabuwar rigima ta kunno kai tsakanin kwamishinan addini na Kano, da wani dalibin Abduljbbar.

Wata sabuwar rigima ta barke tsakanin wani dalibin Abduljbbar da Kwamishinan harkokin addini na jihar Kano, Dakta Tahar Adamu wanda akafi sani da Baba Impossible. Kamar yanda kowa ya sani cewa su Baba Impossible sune sukai tsayin daka wajen ganin cewa an shirya zaman Mukabala tsakanin Malam Abduljbbar da malaman jihar Kano, akan zargin da … Read more

Bidiyo. Ma’aikatar lafiya ta Najeriya zata maka Shek Abdallah Usman Gadon Ƙaya a Kotu.

Wani sabon al’amari ya kunno kai, inda ma’aikatar lafiya ta Najeriya take shirin maka babban malamin Addini Shek Abdallah Usman a Kotu. Malam Abdallah yayi magana ne wadda hukumar lafiyar tace ba zata lamunta ba, wato wani jawabi da malamin yayi akan wata mummunar halayya da yace ma’aikatan asibiti mumamman mata suna aikatawa. Wannan dai … Read more

Bidiyo. Yadda akai wa malamai wulakanci a fadar shugaban kasar Nigeria.

Subhanallah. Anyi wa manyan Malaman Addini wulakanci a fadar shugaban kasar Nigeria, kamar yanda Shek Daurawa ya bada labari. Wannan abu dai bai yi dadi ba. Babban malamin Addini Shek Aminu Ibrahim Daurawa ya bada labarin yanda akai musu wulakanci a fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, a lokacin da aka gayyace su yin wa’azi. … Read more

Shek Ahmad Gumi yayi alwashin bazai kara shiga tsakanin Gwamnatin Najeriya da yan ta’adda ba.

Fitaccen malamin addini mazaunin jihar Kaduna wato Shek Ahmad Gumi, ya fitar da wata zazzafar sanarwa zuwa ga Gwamnatin Najeriya. Duk masu bibiyar al’amuran yau da kullum da suka shafi Najeriya, musamman bangaren Arewa, zasu ga yanda a baya Shek Ahmad Gumi yai ta fafutukar neman sulhu, tsakanin Gwamnatin kasar da yan bindiga. To a … Read more