Bidiyo: Shek Nuru Khalid shine jagora kuma shugaban yan ta’adda a Najeriya. Inji wani malami.

Ana wata ga wata. Wani malami ya kawo wata sabuwar magana, wadda ta saba da fahimtar yawancin yan Najeriya, Inda malamin yake fada cewa Shek Nuru Khalid shine jagoran yan ta’adda a Arewacin Najeriya. Hakika mutane sunyi mamakin wannan magana da malamin yayi, domin kuwa kusan kowa yana kallon Shek Khalid a matsayin wani mutum … Read more

Bidiyo. Jami’an tsaro ne suke ba wa yan ta’adda bindigogi a Arewacin Najeriya. Inji Shek Ahmad Gumi.

Fitaccen malamin Addini, Shek Ahmad Gumi, ya fallasa wata magana mai matukar mahimmanci, inda yake tabbatar da cewa jami’an da ake biyan su domin su kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sune da kansu suke ba wa yan ta’adda bindigogin da suke ta’addanci dasu. Oh! Duniya ina zaki damu? Lamarin Najeriya dai ya gama tabarbarewa da … Read more

Bidiyo. Rigimar Shek Nuru Khalid da Gwamnatin Buhari ta canja salo.

A wannan lokacin dai babu zancen da yake yamutsa hazo a Arewacin Najeriya, kamar maganar korar da Gwamnatin kasar tai wa babban malami Shek Muhammad Nuru Khalid. Kamar yanda kuka sani, korar dai ta biyo bayan wata magana da malamin yayi a yayin da yake gabatar da Huduba a ranar Juma’ar da ta gabata. Inda … Read more

Bidiyo. Ingantacciyar magana akan gwajin cuta kafin aure – Bini Usman.

Hukuncin gwajin cuta kafin aure. Shek Muhammad Bini Usman ya fede biri har wutsiya akan wannan al’amari da yake shige wa mutane duhu. Hakika wannan wata babbar magana ce wadda take bukatar wayar da kan al’umma akai, domin akwai abubuwan da ake aikatawa wadanda ko kadan basu dace ba. Da farko dai zamu iya cewa … Read more

Bidiyo. Yadda akai wa malamai wulakanci a fadar shugaban kasar Nigeria.

Subhanallah. Anyi wa manyan Malaman Addini wulakanci a fadar shugaban kasar Nigeria, kamar yanda Shek Daurawa ya bada labari. Wannan abu dai bai yi dadi ba. Babban malamin Addini Shek Aminu Ibrahim Daurawa ya bada labarin yanda akai musu wulakanci a fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, a lokacin da aka gayyace su yin wa’azi. … Read more

Bidiyo. Malamai sun fara shiga maganar Sarkin Waka, akan ayar dukan mata.

Daga karshe dai malamai sun shiga maganar Naziru Sarkin Waka wadda ta haddasa cecekuce, akan Ayar Qur’anin da tace miji ya daki matar sa. Har yanzu dai wannan cecekuce bai kare ba, domin kuwa har yanzu ana nan ana baje hujjoji akan shafin Instagram na Naziru Sarkin Waka, dan gane da ayar Qur’anin nan da … Read more

Bidiyo. Ansa gasar makuden kudade, ga duk wanda ya rantse cewa Abduljbbar ya zagi Manzon Allah SAW.

Ana wata ga wata, Ansa gasar makuden kudade har dala dubu 5, kusan Naira Miliyan 3 ga duk wanda ya rantse cewa Abduljbbar ya zagi Annabi. Shahararren dan jarida mazaunin kasar Ghana wanda ake kira Mista Fu’ad, shine ya sa wannan gasa mai gwabi. To shidai Abduljbbar har yanzu yana can a kulle a Kurkuku … Read more

Kalaman Abduljbbar, Wadanda suka janyo har akayi Mukabala.

Dalilin wa dalilatan. Yau zamu kawo muku wasu yan bayanai da Abduljabbar yayi a baya, wadanda suka janyo har akayi Mukabala. Hakika bayanan da suka haddasa Mukabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano suna da yawan gaske, sai dai zamu tsakura muku kadan daga cikin dalilan a cikin wannan labarin. Kamar yanda kuka sani, duk malaman … Read more