Bidiyo: Shek Nuru Khalid shine jagora kuma shugaban yan ta’adda a Najeriya. Inji wani malami.

Ana wata ga wata. Wani malami ya kawo wata sabuwar magana, wadda ta saba da fahimtar yawancin yan Najeriya, Inda malamin yake fada cewa Shek Nuru Khalid shine jagoran yan ta’adda a Arewacin Najeriya. Hakika mutane sunyi mamakin wannan magana da malamin yayi, domin kuwa kusan kowa yana kallon Shek Khalid a matsayin wani mutum … Read more

An dakatar da Shek Nuru Khalid daga limanci akan sukar Gwamnati.

Babban malamin Addini Shek Nuru Khalid wanda ake wa lakabi da Dijital Imam ya hadu da fushin gwamnatin Buhari, inda aka dakatar dashi daga limancin masallacin da ya ke jagoranta a Abuja. Shek Khalid dai malami ne wanda yai kaurin suna wajen aika wa gwamnati zafafan sakonni, musamman idan yaga anyi wani abin da bai … Read more

Za’a dakko sojojin haya a Arewacin Najeriya domin magance matsalar tsaro a kasar.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa’i tare da sauran gwamnonin Arewacin Najeriya, suna shirin yin hayar sojoji daga kasashen waje domin magance tashin hankalin rashin tsaro da yaki ci yaki cinyewa. Kuma gwamnanin sun bada sharadin cewa, zasu aiwatar da wannan aiki matukar Gwamnatin Muhammadu Buhari bata dauki matakin da ya dace ba. Bayan gwamnan … Read more

Bidiyo. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Masu garkuwa sun tare mahaifiyar jarumar Kannywood.

Har yanzu dai tsoro da firgici da tashin hankali suna kara hauhawa a zukatan mutanen Najeriya. Musamman ma bangaren Arewan kasar. A daren jiya ne masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna suka tare mutane, ciki harda mahaifiyar daya daga cikin jaruman Kannywood. Wato Samha Nura M Inuwa. Kuma masu garkuwar sun tare su … Read more

Shek Ahmad Gumi yayi alwashin bazai kara shiga tsakanin Gwamnatin Najeriya da yan ta’adda ba.

Fitaccen malamin addini mazaunin jihar Kaduna wato Shek Ahmad Gumi, ya fitar da wata zazzafar sanarwa zuwa ga Gwamnatin Najeriya. Duk masu bibiyar al’amuran yau da kullum da suka shafi Najeriya, musamman bangaren Arewa, zasu ga yanda a baya Shek Ahmad Gumi yai ta fafutukar neman sulhu, tsakanin Gwamnatin kasar da yan bindiga. To a … Read more

Bidiyo. Adam A Zango da Zee Pretty sun bude wa Buhari wuta akan kisan yan Arewa.

Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood Adam A Zango, tare da fitacciyar jaruma Zee Pretty, sun rufe ido sun bude wa shugaban kasar Najeriya wuta. Jaruman Kannywood sun fara fusata akan halin da kasar Najeriya take ciki, musamman bangaren Arewacin kasar. Inda wasu daga cikin jarumai suka fara bude baki, domin shugabanni su gaggauta daukar mataki. … Read more

Bidiyo. ‘Yan Arewacin Najeriya sun shiga zanga-zanga, akan rashin tsaro.

Tura ta fara kaiwa Bango. Mutane a Arewacin Najeriya sun fara zanga-zanga, saboda halin da ake ciki na rashin tsaro a kasar. Hakika wannan babban al’amari ne, domin yanda ake kashe mutane a Arewacin Najeriya, abin ya wuce gona da iri. Kusan zamu iya cewa tun lokacin mulkin tsohon shugaban ‘kasa Good Luck Ebele Jonathan … Read more

Yanda ake cinikin kudin fansa da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara.

babbaka. Tsoro da firgici yana kara hauhawa a zukatan yan Najeriya, a inda har yanzu masu garkuwa da mutane suke ci gaba da cin karen su babu babbaka. Hakika wannan mummunan al’amari kawai sai dai ace Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Babban abinda har yanzu aka rasa amsar sa shine. Shin wai ina hukumomin tsaro? … Read more

Bidiyo. “Lokacin mutuwa ta ne yazo, shiyasa har aka kamani.” Cewar wani Bafulatani.

Dubun wani dan ta’addan Bafulatni ta cika, inda ya shiga hannun jami’an tsaro, kuma ya lissafo duk munanan laifukan da yake aikatawa. Har yanzu dai idan akace Najeriya, abu na farko da yake zuwa zuciyar mutane shine satar mutane da yin garkuwa dasu. Kuma ana ji ana gani, Fulani sunyi ‘kaurin suna akan wannan mummunar … Read more

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Yanzuyanzu, an sace wata yarinya mai suna Haneefa a jihar Kano.

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, duniya ina zaki damu? Yanzu-yanzu wasu marasa imani sun sace wata yarinya. Mutane sun shiga alhini da tashin hankali a jihar Kano, inda wani barawo mara imani yazo da mashin mai taya 3 (Keke napep) ya sace wata karamar yarinya. Wannan abin alhini dai ya faru ne a karamar hukumar … Read more