Bidiyo. Rigimar Shek Nuru Khalid da Gwamnatin Buhari ta canja salo.

A wannan lokacin dai babu zancen da yake yamutsa hazo a Arewacin Najeriya, kamar maganar korar da Gwamnatin kasar tai wa babban malami Shek Muhammad Nuru Khalid. Kamar yanda kuka sani, korar dai ta biyo bayan wata magana da malamin yayi a yayin da yake gabatar da Huduba a ranar Juma’ar da ta gabata. Inda … Read more

Shin wai AA Zaura ne yake neman kujerar Gwamnatin Kano, ko kuma kujerar Gwamnatin Kano ce take neman AA Zaura?

Banbancin dake tsakanin AA Zaura da sauran yan takarar Gwamna a Kano. Mai neman fadar gaskiya dole ne yaji tsoron Allah, sannan kuma ya zama wajibi ya zurfafa bincike domin tabbatar da cewa gaskiyar ce tsantsa ta fito daga bakin sa. Hakika talakawa da yawa a Najeriya ba iya a Kano a kadai ba sun … Read more

Bidiyo. A karon farko Ganduje ya yaba wa kokarin Kwankwaso.

Gwamnan jihar Kano mai ci a yanzu Abdullahi Umar Ganduje ya yaba wa kokarin tsohon Gwamnan wato Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso. Da alama dai adawar siyasa bata dorewa har abada, domin kuwa wasu lokutan duk tsananin gabar dake tsakanin yan siyasa sai kawai wataran kaga sun gyaro ta, tamkar babu abinda ya faru a baya. … Read more

Najeriya tana bukatar yawaitar yan tawaye, domin samun ci gaba. Cewar Obasanjo.

Tsohon shugaban kasar ta Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya kawo wani sabon al’amari, inda ya bada shawarar cewa ya kamata a samu karin yan tawaye masu yawan gaske a kasar, wandanda basuda tsoro. Wato wadanda duk rintsi duk wuya zasu iya tsayawa a gaban shugaba su bude baki su gaya masa gaskiya ba tare da … Read more

Bidiyo. Mawakan Kano sun fara fusata akan wani abu da Rarara ya aikata.

Mawakan jihar Kano sun fara kosawa kuma sun fara fusata akan wani alkawari da fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya dauka. Yau dai kusan watanni goma kenan da Rarara ya kawo wata babbar gasa tsakanin mawaka na kowanne fanni, wato mawakan gargajiya, da mawakan Hausa Hip-hop da kuma mawakan fina-finai na Hausa. Inda aka … Read more

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai sayar da kamfanonin kasar har guda 42.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki aniyar siyar da wasu kamfanoni mallakin kasar har guda 42 mallakin Gwamnati. Hukumar sayar sa kadarorin kasar wato NCP, wadda mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ke jagoranta, itace ta bada umarni ga hukumar kula kamfanonin gwamnati wato BPE, dangane da batun cefanar da kamfanonin. A halin yanzu dai gwamnati zata … Read more